Saturday, May 9, 2020

Bude YouTube Channel

YADDA AKE BUDE YOUTUBE CHANNEL


A cikin kasidarmu da ta gabata, mun kawo muku sharhi akan hanyoyi guda ukku da zasu fi kawo kudi a shekarar 2017. A cikin wadannan hanyoyi guda ukku, mun yi Magana akan yadda ake samun kudi da YouTube, ta hanyar sanya Videos wadanda idan mutane da yawa suka kalla, to kaima za’a baka wasu ‘yan kudi. A cikin wannan kasidar, zamu yi muku bayani akn yadda zaku bude YouTube channel, wanda da shine zaku yi amfani wajen dora Videos dinku a saman youtube din.

Idan kana bukatar shiga fagen samin kudi ta hanyar YouTube to farko abin da za ka yi shine ka tabbatar ka mallaki hanyar da zaka iya karbar kudi ta internet (za mu yi bayani akan hakan nan gaba kadan).


Bayan ka mallaki  wannan account, abu na gaba da kake bukatar yi shine ka mallaki YouTube channel.

Domin mallakar YouTube channel, sai ka bi wadannan matakan:

Ka fara bude Google account ko kuma Gmail (Shiga nan don ganin yadda ake bude gmail)
Sai ka shiga YouTube (idan son samu ne kayi amfani da computer don yafi sauki)
Bayan ka shiga sai ka je daga can saman page gefen dama (idan da computer kake amfani), ko kuma can kasan page din (Idan da waya kake amfani), zaka ga inda aka sanya sign in, sai ka shiga nan.
Da ka shiga sign in za ga inda za ka sanya Username da password, sai ka sanya gmail address naka a matsayin username, da kuma password dinka da kayi amfani da shi wajen bude gmail din. Idan ka sanya komai dai-dai, wannan zaya ko ma da kai a page din YouTube.
Idan da computer kake amfani, sai ka duba daga banagaren hagu akwai waya ‘yar alama sai ka taba ta. Wannan zaya buda maka zabukan da ke a gurin, sai ka shiga ‘My Channel’

Da ka shiga ‘My Channel’ zaka ga wani page da za ya bukaci kayi setting na Channel dinka (kamar sunan channel din dai sauransu)

Da zaran ka shiagar da bayananka sai ka sanya create.

Wadannan sune matakan da kake bukata domin bude channel ko kuma tasharka a shafin YouTube. A cikin kasidarmu ta gaba, in Allah ya so, za mu yi Magana akan yadda zaku iya dora videos a saman wannan channel naku na YouTube.



Idan kana bukatar tofa albarkacin bakinka game da wannan kasidar, ko kuma kana da wata tambaya to karka yi wata-wata kayi comment a nan kasa. Ga duk mai bukatar samun kasidunmu ta hanyar Whatsapp shima ya iya yin comment da lambarshi.
MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL

2 comments:

  1. আমি মোঃরকি ইসলাম । পেশায় একজন প্রবাসি। বর্তমানে মালেশিয়ায় বসবাস করছি। ব্লগ পড়তে ও আর্টিকেল লিখতে পছন্দ করি
    sad dp
    Sad status in hindi
    LOVE QUOTES IN HINDI
    what is love?
    font copy and paste
    অনলাইন কাজ

    ReplyDelete