Saturday, May 9, 2020

Wani Sojan Najeriya Ya Fasa Kwai!!!

Wani sojan Najeriya a jihar Borno yayi zargin cewar a gaban idonsu 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan garin Gamboru-Ngala inda suka kashe mutane har 300, amma kwamandansu yaki ba su Umarnin kai dauki.
Sojan wanda muka boye sunansa ya ce ko baya ga su sojan kasa har da jirgin saman yaki ya zo yana shawagi a sararin samaniya garin a lokacin da harin ke gudana amma ba a bashi umarnin kai harin ba.
Da ma wadanda suka tsira daga harin na Gamborun Ngala sun nemi da a janye sojojin daga garin saboda a cewarsu ba su yi musu wata rana ba sa'adda harin ke gudana.
Sojan ya kara da cewa su na zargin wannan hari da aka kai na hadin baki ne, saboda rashin hana su aiwatar da aikinsu.
Haka nan 'yan kato da gora da ke aiki a cikin Gamboru Ngala sun shaida musu cewa maharan ba su zo da makamai masu yawa ba.
Sojan yace idan har manyan su ba su cire hannunsu a harkar Boko Haram ba to kuwa ba za ayi nasara ba a yaki da ake yi da kungiyar.
SOURCE: BBC HAUSA!
Hmmmmn ko yaushe ne zamu gane cewa da sa hannun gwamnatin tarayya akashe mana mutane? Mu idan munyi maganar hakan sai 'yan wawaye suyi fiki - fiki suna kare gwamnatin mai malafa sbd kawai wai jam'iyarsu daya, jam'iyar BANZA DAN UBANTA...!
Naga alama sokuke sai kunga mai malafa kiri - kiri da bindiga yana harbemu sannan zaku farga kudena sonsa, sai anyi magana kuce ai saboda kuna GABA da wasu gwamnoni ne shiyasa kuka gwammace kutare awajen mai kashemu, ina ruwanku da gwamnonin, can zasu yanka suma takansu suke dan haka muma da ake kashewa dole ne mucire waje daya.
Mukam wlh siyasa bata dace damuba, bamu iyataba kuma bazamu iya ba har abada!
Allah ya agazamana ya kuma hada kawunanmu koda jagororinmu basaso, domin hadin kanmu wani babban tangardane awajensu musamman wajen cinma burikansu na SIYASA.
MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL

No comments:

Post a Comment