Saturday, May 9, 2020

Yadda Ake Amfani da Kowanne Layi Akan Modem Daya Batareda Anyi Unlock ba

YADDA ZAKA YI AMFANI DA KOWANNE
LAYI AKAN MODEM DAYA BA TARE DA
UNLOCK BA.
Kasan cewar masu amfani da computer,
sukan yi amfani da layi daya kacal akan
modem dinsu, amma kuma suna bukatar
canza layi, suna tunanin sai sunyi unlock
sannan hakan zata kasance ya dauki wani
layi.
To wannan hanya ce da zata baka damar amfani da modem daya akan
layikanka na waya batare da kayi mata
unlock ba hanya mafi sauki, da zaka yi aiki
na yadda zaka meda modem dinka ta
dauki ko wanne layi akanta ba tare da
unlock ba.
Ya na da kyau ka mallaki Nokia PC suite akan computer ka sannan wannan
bayani zai zama mai amfani a gareka
sannan ka bi wadannan hanyoyin
YADDA AKE SA WANI LAYIN AKAN MODEM
BATARE DA UNLOCK BA.
Da farko ka tabbatar ka sauko da Nokia
PC Suite akan Kwamfutar ka ta hanyar
aziyartar shafinsu ko kuma yin amfani da
google search domin nemo shi akan PC
dinka.
Kasa ko wanne irin layi akan PC naka wacce bakai mata unlock din ba, sannan ka
jona shi da kwamfutar ka.
Kana sawa software na modem naka zai
garga deka da cewa INVALID SIM CARD
kawai kayi banza da shi, ka wuce karka
damu ka rufe modem Software naka ka kulle shi kawai.
Bayan ka kulle modem software naka
saika je ka bude Nokia PC Suite wanda ka
sauko da shi kan PC taka.
Bayan ka bude Nokia PC Suite saika latsa
''File'' ka zabi ''Connetion to the Internet'' sannan ka latsa spanner Icon dan tabbatar
da setin sa, wato seta layin da kasa akai.
Saika zabi modem naka daga jerin
abubuwan da aka jero maka, sannan kasa
seti na layin da kasa kamar yadda kake
seta waya, wato kasa ''Access Point Name (APN)'' na sunan layin da kasa akai dan yin
seti
MISALI: kasa MTN ko Etisalat Ko Airtel
Ko glo Nigeria, duk wanda kasa daga ciki
saika sa APN na kamfaninsa, Misali:
MTN NEGERIA
APN: web.gprs.mtnnigeria.com.ng
ETISALAT NIGERIA
APN: etisalat
GLO NIGERIA
APN: glowap
AIRTEL NIGERIA
APN: internet.airtel.com.ng
Indai kasa na layinka wanda kasa ka
gama seti na wannan layi akan modem
naka marar unlock
Saika danna Connect ta cikin Nokia PC
Suite naka nan take zai hada ka da yanar
gizo ba tare da bata lokaci, ka hada SIM CARD naka da modem ba tare da kayi
unlock nata ba.
Zata dauki duk wani layi
basai nata kadai ba.
SANARWA Zaka iya sa wani layi kuma bayan wanda
kasa idan kabi hanyar da ka karanta a
sama, kar kayi tunanin idan ka seta layi
daya to kowanne kasa zaiyi, misali karka
seta MTN sannan ka cire kasa Etisalat kace
zaiyi ba tare da ka sake biyo wa yadda kayi na wancan ba, kuma karka sa setin na MTN
kace zakayi da Etisalat ko makamancin
haka, ko wanne layi na kamfani daban, to
setinsa daban yake, Sai akiyaye.
 By: MUSA SIDI 
 09012975820; 08116630698

No comments:

Post a Comment