Saturday, May 9, 2020

Bude YouTube Channel

YADDA AKE BUDE YOUTUBE CHANNEL


A cikin kasidarmu da ta gabata, mun kawo muku sharhi akan hanyoyi guda ukku da zasu fi kawo kudi a shekarar 2017. A cikin wadannan hanyoyi guda ukku, mun yi Magana akan yadda ake samun kudi da YouTube, ta hanyar sanya Videos wadanda idan mutane da yawa suka kalla, to kaima za’a baka wasu ‘yan kudi. A cikin wannan kasidar, zamu yi muku bayani akn yadda zaku bude YouTube channel, wanda da shine zaku yi amfani wajen dora Videos dinku a saman youtube din.

Idan kana bukatar shiga fagen samin kudi ta hanyar YouTube to farko abin da za ka yi shine ka tabbatar ka mallaki hanyar da zaka iya karbar kudi ta internet (za mu yi bayani akan hakan nan gaba kadan).


Bayan ka mallaki  wannan account, abu na gaba da kake bukatar yi shine ka mallaki YouTube channel.

Domin mallakar YouTube channel, sai ka bi wadannan matakan:

Ka fara bude Google account ko kuma Gmail (Shiga nan don ganin yadda ake bude gmail)
Sai ka shiga YouTube (idan son samu ne kayi amfani da computer don yafi sauki)
Bayan ka shiga sai ka je daga can saman page gefen dama (idan da computer kake amfani), ko kuma can kasan page din (Idan da waya kake amfani), zaka ga inda aka sanya sign in, sai ka shiga nan.
Da ka shiga sign in za ga inda za ka sanya Username da password, sai ka sanya gmail address naka a matsayin username, da kuma password dinka da kayi amfani da shi wajen bude gmail din. Idan ka sanya komai dai-dai, wannan zaya ko ma da kai a page din YouTube.
Idan da computer kake amfani, sai ka duba daga banagaren hagu akwai waya ‘yar alama sai ka taba ta. Wannan zaya buda maka zabukan da ke a gurin, sai ka shiga ‘My Channel’

Da ka shiga ‘My Channel’ zaka ga wani page da za ya bukaci kayi setting na Channel dinka (kamar sunan channel din dai sauransu)

Da zaran ka shiagar da bayananka sai ka sanya create.

Wadannan sune matakan da kake bukata domin bude channel ko kuma tasharka a shafin YouTube. A cikin kasidarmu ta gaba, in Allah ya so, za mu yi Magana akan yadda zaku iya dora videos a saman wannan channel naku na YouTube.



Idan kana bukatar tofa albarkacin bakinka game da wannan kasidar, ko kuma kana da wata tambaya to karka yi wata-wata kayi comment a nan kasa. Ga duk mai bukatar samun kasidunmu ta hanyar Whatsapp shima ya iya yin comment da lambarshi.
MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL

[Blogging] Hanyoyi 6 da Zaka Sanya Mutane Su Dinga Shiga BLOG Dinka.

[Blogging] Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

A yau zanyi magana akan wasu hanyoyi guda 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga blog dinka a koda yaushe.

Ka dinga wallafa bayanan masu amfani da shafinka, idan akayi maka comment na yabawa to kayi kokarin wallafashi domin wanda yayi zaiji dadi, sannan suma masu bibiyarka zasu kara samun gamsuwa da kai, sannan ka basu damar bayyana ra’ayoyinsu a comment.
Ka dinga yin reply ga masu aikowa da shafinka sakonni ta comment ko inbox.
Ka dinga yin sharing tsoffin postin misali yau nayi magana akan Yadda ake satar account din facebook to akwai bukatar lokaci zuwa lokaci ka kara dawo dashi domin ka samu sabbin abokai an samu karin wanda basu karantashi ba a baya, wannan ga irin namu Bloggers din kenan ba masu Blog din Labarai ba.
Ka dinga shirya zabe ko kacici-kacici/tambaya idan anci kayi yabo ko ka saka kyauta, wannan zai kara jawo maka hadin kan jama’a sosai, misali kwanaki shafinmu na Jaridar Tsanya ya sanya gasar cewa duk wanda ya fadi inda aka dauki wasu hotuna da ya wallafa za’a bashi 1,500  haka aka samu wata daliba ta amsa kuma aka bata kyautar, hakan ya janyowa shafin tarin jama’a sosai.
Kada ka dinga wallafa rigingimu a shafunka, musamman rigingimun addini ko na kabilanci da makamantansu ka maida hankali kan iya abinda shafinka ya sanya gabam ka guji wallafa koda ra’ayinka na siyasa, misali a shafin com na internet da su Facebook bamu taba wallafa wani ra’ayinmu akai ba idan zamuyi wannan sai muyi amfani da personal account dinmu, haka akeso.
Ka baiwa masu ziyarar shafinka damar suyi subscribing ta email ta yadda kana wallafa abu zasu gani a email dinsu, sannan ka gayyacesu zuwa sauran shafukanka na social media.
Allah ya taimaka.
 MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL ™️
08116630698; 09012975820

THE HISTORY

In The History Of The World Who Has Killed Maximum Innocent Human Beings???
1) "Hitler" Do You Know Who Was He????? He Was a Christian, But Media Will Never Say That Christians Are
Terrorist!!!!!
2) Joseph Stalin Called As Uncle Joe "He Has Killed 20 Million Human Beings Including 14.5 Million Were Starved To Death" Was He Muslim???
3) Mao Tse Tsung (China)
"He Has Killed 14 To 20 Million Human Beings." Was He Muslim???
4) Benito Mussolini (Italy)
"He Has Killed 400 Thousand Human Being, Was He Muslim???
5) Ashoka "In Kalinga Battle He Has Killed 100Thousand
Human Being, Was He Muslim???
6) Embargo Put By George Bush In Iraq 1/2 Million Children Has Been Killed In Iraq
Alone!!!
Imagine This People Are Never Called Terrorist By The Media. Why??? Today The Majority Of The Non Muslims Are Afraid
By Hearing The Words "Jihad" Jihad Is An Arabic Word Which Comes From Root Arabic Word "Jahad" Which Means "To Strive" Or "To Struggle"
"To Strive Or Struggle" Against Evil And For
Justice, It Does Not Mean Killing Innocents,The
Difference is We Stand Against Evil , Not With Evil". Share As Much As u Can !!!
You still think that ISLAM is the problem???
1. The First World War 17 Million dead (caused by non-Muslim)
2. The Second World War 50-55 Millions dead (caused by non-Muslim)
3. Nagasaki atomin bombs 200000 dead (caused by non-Muslim)
4. The War in Vietnam over 5 Million dead (caused by non-Muslim)
5. The War in Bosnia/ Kosovo over 500000 dead (caused by non-Muslim)
6. The War in Iraq (so far) 1,2000,000 deaths (caused by non-Muslim)
7. Afghanistan, Burma etc (caused by non muslim)
In cambodia 1975-1979 almost 3 million deaths (caused by non muslim )
SHARE & COPY PLEASE!
 MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL
08116630698

Wani Sojan Najeriya Ya Fasa Kwai!!!

Wani sojan Najeriya a jihar Borno yayi zargin cewar a gaban idonsu 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan garin Gamboru-Ngala inda suka kashe mutane har 300, amma kwamandansu yaki ba su Umarnin kai dauki.
Sojan wanda muka boye sunansa ya ce ko baya ga su sojan kasa har da jirgin saman yaki ya zo yana shawagi a sararin samaniya garin a lokacin da harin ke gudana amma ba a bashi umarnin kai harin ba.
Da ma wadanda suka tsira daga harin na Gamborun Ngala sun nemi da a janye sojojin daga garin saboda a cewarsu ba su yi musu wata rana ba sa'adda harin ke gudana.
Sojan ya kara da cewa su na zargin wannan hari da aka kai na hadin baki ne, saboda rashin hana su aiwatar da aikinsu.
Haka nan 'yan kato da gora da ke aiki a cikin Gamboru Ngala sun shaida musu cewa maharan ba su zo da makamai masu yawa ba.
Sojan yace idan har manyan su ba su cire hannunsu a harkar Boko Haram ba to kuwa ba za ayi nasara ba a yaki da ake yi da kungiyar.
SOURCE: BBC HAUSA!
Hmmmmn ko yaushe ne zamu gane cewa da sa hannun gwamnatin tarayya akashe mana mutane? Mu idan munyi maganar hakan sai 'yan wawaye suyi fiki - fiki suna kare gwamnatin mai malafa sbd kawai wai jam'iyarsu daya, jam'iyar BANZA DAN UBANTA...!
Naga alama sokuke sai kunga mai malafa kiri - kiri da bindiga yana harbemu sannan zaku farga kudena sonsa, sai anyi magana kuce ai saboda kuna GABA da wasu gwamnoni ne shiyasa kuka gwammace kutare awajen mai kashemu, ina ruwanku da gwamnonin, can zasu yanka suma takansu suke dan haka muma da ake kashewa dole ne mucire waje daya.
Mukam wlh siyasa bata dace damuba, bamu iyataba kuma bazamu iya ba har abada!
Allah ya agazamana ya kuma hada kawunanmu koda jagororinmu basaso, domin hadin kanmu wani babban tangardane awajensu musamman wajen cinma burikansu na SIYASA.
MUSA SIDI ZAGGA OFFICIAL

YADDA ZAKA SAMI N30,000 CREDIT AKAN LAYIN ETISALAT DINKA DOMIN KIRAN DUKKAN LAYIKAN NIGERIA A KYAUTA……

GA MATAKAN DA ZAKA BI DOMIN YIN ACTIVATING DIN LAYINKA DOMIN SAMUN WANNAN BONUS KO KUMA INCE FREE CALL:
MATAKI NA 1: Ka sami simcard guda 2 na etisalat ko kuma ka aro guda daya
daga wajen abokinka sannan sai ka hada da naka kenan sun zama guda biyu kenan....
MATAKI NA 2: Ka tabbata wannan layin da ka aro yana yin FREE CALL idan kuma bayayi sai kayi activating dinsa.
MATAKI NA 3: Ka sami wata waya daban sai ka sanya wannan layin daka aro din a ciki wayar sannan sai kuma layin naka shima ka sanya shi a waya daban... Amma ka tabbab ko wace wayar kayi mata full charge kafin ka fara..
MATAKI NA 4: Shikenan da misalin karfe 
12:40 a.m na dare kenan lokacin mid night call, sai kayi amfani da wannan sim din daka aro saika kira wannan layin naka idan ta fara RINGS sai dauki kiran sai ka kyaleta tayi 5 MINS sannan saika yanke kiran....
MATAKI NA 5: Bayan ka yanke kiran sai kuma kara kiran lambar taka AGAIN nan sai ka dauki kiran ka barta tayi wata minti biyar din saika yanke kiran.
MATAKI NA 6: Nan ma sai ka sake kiran a karo na uku amma a wannan lokacin zaka bar wannan kiran ne domin anan ne zakayi ACTIVATED DIN SIMCARD DINKA.
SHAWARA: Wadannan wayoyin guda biyu kasanya su chaji domin karda battery dinka ya dauke, sannan saika kwanta ka shari barcinka.
MATAKIN KARSHE: Zaka tashi ne daga barcin da misalin karfe 4:30 a.m na safe domin ka yanke kiran da layi tun a free call sannan saika danna *232# kaga abin mamaki a acct dinka and s
( 20,000 naira bonus )
WULD BE CREDITED TO YOUR BALANCE TO CALL ANY
NETWORK FREE
tested and confirmed.
WhatsApp Contact For More Info:
+2349012975820
Daga:
Musa Sidi.

Yadda Zaka Samu 1,000 Airtime Kyauta A Layin MTN

SAMU KYAUTAR N1,000 AIRTIME A LAYIN MTN KYAUTA...
Wannan garabasar ta kan samu ne a layin MTN wanda aka ajiye a kasa har tsawon wata daya ko sama ba'a yi amfani dashi ba......
To idan kana da layin da ka ajiye kayi sauri ka kakkabeshi da loda masa katin N100 kacal zaka samu wannan garabasar ta N1,000 kyauta wanda zaka kira layikan MTN har na tsawon Sati daya....
Dear customer, if you have any MTN SIM that you have not used for a month or more , put it in your phone now and get N1000 FREE airtime when you recharge...
WhatsApp contact:
+2349012975820
Call: +2348116630698
Daga:-
MUSA SIDI ZAGGA

Yadda Zaka Kara Saurin Internet Na 2G, 3G, 4G, Wi-Fi Akan Wayar Android

YADDA ZAKA KARA SAURIN INTERNET NA 2G, 3G, 4G, WIFI AKAN WAYAR ANDROID.

Daga:- MUSA SIDI OFFICIAL ™️

Kuna Tare Da Musa Sidi.

Yanxu da gaggawa ina son in gabatar maku da wani application mai suna Faster Internet
2x. Wannan app ne na wayar android app wanda zai taimake ka wajen kara saurin Internet bakamar yadda yake ba. 

Wannan app din yana da wata dama ta kara maka saurin browsing.kuma yana improve na
signal reception.

Yana aiki akan kowace waya da wadda akayi ma rooting da kuma wanda ba'ayi rooting ba.
Amma dai zaifi aiki kwarai ga wayar da kayi ma rooting.

Saboda Me Zanyi Amfani Da Faster Internet App?

1. Domin ya kara ma network karfi.

2. Zai kara ma internet browsin sauri ba kamar da ba.

3. Yana aiki akan wayar android da kayi ma rooting da wadda ba'a yi ma rooting.

4. Kuma baya jan battery gaba daya.

A Ina Zanyi Download Wannan App?

==> Yi Download Dinshi Anan

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.james.fasterinternet&hl=en

=> Sai kayi Run da install dinsa akan wayarka.

=> Ka Latsa wajen start button domin kara gudun 2G, 3G da
4G internet speed.

Shikenan Cigaba Da Browsing Sharp_Sharp Domin Na GwadaShi Kuma Yana Aiki Normal.

Idan Ka Tambaya Sai Kayi Akan Wannan App.
Kuma Kayi Comment,Like Da Share Domin Friends Dinka Su Gani Su Karu.

Daga:- MUSA SIDI
MUSA SIDI ZAGGA Wizard.
09012975820; 08116630698

Shin Ana Iya Leƙen Asirin Mutum Ta Waya Kuwa?

Amsa itace ‘e’ ana iyawa, domin mafi yawancin mutane da ke amfani da manyan wayoyi (smartphone) irin su Android, iPhone, iPad da mkamantansu tamkar kusan tsirara suke. Akwai mutane da kan iya ganin sirrin ka ta cikin wayar taka daga nesa. Babban abu ma shi ne akwai waɗansu Apps da idan ka sake ka sa su a wayar ka za su fara aiki a boye (background) kai tsaye har ma da amsa kuwar ɗin wayar ka (microphone) ta ɗaukar maganganun ka tana aika wa da su. Ƙarami daga cikin irin waɗannan Apps ɗin shi ne stealthGenie (spyware) yakan zama abin da ake cewa Trojan kuma yana iya aiki da iOS dinka, kai hasali ma yakan yi amfani a Android da Blackberry ya aika taswirar (geolocate) ɗinka ya kuma saurari maganganunka, saƙonnin rubutu (text messages) da hotunan ka ya aika da su kowane lokaci.
Wani kamfanin da ya ke yin irin waɗannan Apps sun taɓa yin alfaharin cewar suna da mutane (customers) sama da dubu ɗari (100,000) duk da dai hukumar tsaro a Amurka ta cafke shi shugaban wannan kamfanin.
Za mu iya tunawa da maganganu da ɗan leƙen asirin nan na Amurka wato Edward Snowden da ya yi na cewa gwamnatin Amurka tana leƙen asirin cikin wayoyi, saƙonnin e-mail da sauransu al’amuran intanet na mutane da yawa a cikin duniya. Wannan magana ta tsohon jami’in CIA ta tabbatar mana cewar lallai NSA na amfani da hanyoyi daban-daban wajen neman sirrin mutane.
Akwai wani Apps da ake kira da suna Angry birds shi ma yana ɗaya daga cikin Apps da ake amfani da shi wajen leken asirin.
Saboda haka nake ganin ma cewar ka kiyaye zuwa banɗaki da wayar (smartphone) domin tana iya maka tonan silili.
Masu bincike a jami’ar Stanford sun gwada wani Apps (Gyrophone) domin tabbatar da irin wannan zargin kuma sun ta gano cewar lallai amsa kuwar waya (microphone) kan iya aika sautinka, kai har ma da gano wanda ke yin magana. Wannan Apps na da ƙarfin tafiya a iska na 80 – 250 Hz a kan iska.
Sun gano da tabbatar wa duniya cewar amfani da wannan Apps (Gyrophone) za a iya gano mai magana dama mai amsa maganar. Sun gwada a kan wayar Android ya yi aiki yanzu ma har sun fara gwadawa a kan iPhone.
Wasu jami’oi ma kamar Citizen lab a jami’ar Toronto sun yi wannan gwajin da gano masu leƙen asiri ta irin wannan hanyar a ƙasar Italiya. An tabbatar cewar masu leƙen asirin suna amfani da GPS tracker na amsa kuwarka da zaran ka hau yanar gizo (internet) ta Wi-fi.
Binciken ya nuna cewar akwai manyan kwamfutocin da ake amfani da su wurin leƙa sirrin mutane (computer servers) sama da guda 350 a ƙasashen duniya guda 40 da ake amfani da su. Abin tambaya a nan shi ne, gwamnatocin sun san da haka kuwa? Idan ko sun sani ke nan su ma suna leƙen asirin wayar mutanensu.
Saboda haka ka lura domin wayar ka ta smartphone da kake tunƙaho da ita kake maƙale da ita kullum da guje wa kaɗaici mai tona ma ka asiri ce. Saboda haka abin sai addu’a.
 Daga naku MUSA SIDI ™️📲
 09012975820; 08116630698

Yadda Ake Amfani da Kowanne Layi Akan Modem Daya Batareda Anyi Unlock ba

YADDA ZAKA YI AMFANI DA KOWANNE
LAYI AKAN MODEM DAYA BA TARE DA
UNLOCK BA.
Kasan cewar masu amfani da computer,
sukan yi amfani da layi daya kacal akan
modem dinsu, amma kuma suna bukatar
canza layi, suna tunanin sai sunyi unlock
sannan hakan zata kasance ya dauki wani
layi.
To wannan hanya ce da zata baka damar amfani da modem daya akan
layikanka na waya batare da kayi mata
unlock ba hanya mafi sauki, da zaka yi aiki
na yadda zaka meda modem dinka ta
dauki ko wanne layi akanta ba tare da
unlock ba.
Ya na da kyau ka mallaki Nokia PC suite akan computer ka sannan wannan
bayani zai zama mai amfani a gareka
sannan ka bi wadannan hanyoyin
YADDA AKE SA WANI LAYIN AKAN MODEM
BATARE DA UNLOCK BA.
Da farko ka tabbatar ka sauko da Nokia
PC Suite akan Kwamfutar ka ta hanyar
aziyartar shafinsu ko kuma yin amfani da
google search domin nemo shi akan PC
dinka.
Kasa ko wanne irin layi akan PC naka wacce bakai mata unlock din ba, sannan ka
jona shi da kwamfutar ka.
Kana sawa software na modem naka zai
garga deka da cewa INVALID SIM CARD
kawai kayi banza da shi, ka wuce karka
damu ka rufe modem Software naka ka kulle shi kawai.
Bayan ka kulle modem software naka
saika je ka bude Nokia PC Suite wanda ka
sauko da shi kan PC taka.
Bayan ka bude Nokia PC Suite saika latsa
''File'' ka zabi ''Connetion to the Internet'' sannan ka latsa spanner Icon dan tabbatar
da setin sa, wato seta layin da kasa akai.
Saika zabi modem naka daga jerin
abubuwan da aka jero maka, sannan kasa
seti na layin da kasa kamar yadda kake
seta waya, wato kasa ''Access Point Name (APN)'' na sunan layin da kasa akai dan yin
seti
MISALI: kasa MTN ko Etisalat Ko Airtel
Ko glo Nigeria, duk wanda kasa daga ciki
saika sa APN na kamfaninsa, Misali:
MTN NEGERIA
APN: web.gprs.mtnnigeria.com.ng
ETISALAT NIGERIA
APN: etisalat
GLO NIGERIA
APN: glowap
AIRTEL NIGERIA
APN: internet.airtel.com.ng
Indai kasa na layinka wanda kasa ka
gama seti na wannan layi akan modem
naka marar unlock
Saika danna Connect ta cikin Nokia PC
Suite naka nan take zai hada ka da yanar
gizo ba tare da bata lokaci, ka hada SIM CARD naka da modem ba tare da kayi
unlock nata ba.
Zata dauki duk wani layi
basai nata kadai ba.
SANARWA Zaka iya sa wani layi kuma bayan wanda
kasa idan kabi hanyar da ka karanta a
sama, kar kayi tunanin idan ka seta layi
daya to kowanne kasa zaiyi, misali karka
seta MTN sannan ka cire kasa Etisalat kace
zaiyi ba tare da ka sake biyo wa yadda kayi na wancan ba, kuma karka sa setin na MTN
kace zakayi da Etisalat ko makamancin
haka, ko wanne layi na kamfani daban, to
setinsa daban yake, Sai akiyaye.
 By: MUSA SIDI 
 09012975820; 08116630698